Sojin Sama sun kaiwa Boko Haram goron sallah

Sojin Sama sun kaiwa Boko Haram goron sallah

- Sojin Saman Najeriya suna cigaba da samun taka muhimmiyar rawa a yakin da akeyi da 'yan ta'ada a arewa maso gabashin Najeriya

- Rundunar Sojin Sama na Operation Dole suna daya daga cikin wadanda suka fi jajircewa wajen karyan lagwan yan Boko Haram

- Sojin Saman sunyi sun sami nasarar halaka wasu 'yan ta'adda a Parisu da Takwala duk a Jihar Borno.

A jiya Juma'a 15 ga watan Yuni ne Rundunar Sojin Sama na Operation Dole suka sami nasarar kai wata hari da tayi sanadiyyar halaka wasu yan Boko Haram a garuruwa Parisu da Takwala dake Jihar Borno.

Legit.ng ta gano cewa an kai simamen ne bayan sashin leken asiri na sojin saman sunyi amfani da na'urar bincike sun gano cewa akwai 'yan ta'ada a wuraren biyu.

Sojin Sama sun kaiwa Boko Haram goron sallah
Sojin Sama sun kaiwa Boko Haram goron sallah

KU KARANTA: Gwamna Yari ya yi murabus a mukaminsa na babban mai tsaron jiharsa

Bayan haka ne dakarun sojin saman su kayi amfani da jiragen yaki kirar Alfa Jet dauke da bama-bamai da alburusai kuma suka nufi wuraren su kayi musu luguden wuta.

"Bayan jiragen sun gama yi musu luguden wutar, sauran sojojin dake kasa sun kuma karasa wuraren inda suka halaka burbushin yan ta'adan da suka buya a wasu wurare yayin da ake luguden wuta," inji wata sanarwa da ta fito daga bakin Kakakin hukumar sojin saman, Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya.

Sanarwan kuma ta ce "Sojin saman Najeriyan za su cigaba da amfani da dukkan na'urorin leken asirinsu don gano wuraren da sauran yan ta'adan Boko Haram ke buya don a samar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas."

A wata labarin, Legit.ng ta kawo muku cewa hukumar sojin Najeriya ta gina wuraren saukan jirgin mai saukan angulu guda biyu don inganta harkokin tsaro a jihar.

An kaddamar da wuraren saukan jirgin mai saukan angulun biyu ne a jiya Alhamis 13 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164