Jami'in 'Dan sanda ya Farauci wani 'Dan Kabu-Kabu har Mutuwar sa kan Cin Hanci Na N100 a Jihar Anmabra
Wani karamin ma'aikacin dan sanda a birnin Onitsha dake jihar Anambra, ya yi sanadiyar mutuwar wani dan Kabu-Kabu, Samuel Agu, wanda bai wuci shekara 22 a duniya ba.
Lamarin dai kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana ya afku ne yayin da jami'in dan sandan ya bi Marigayi Samuel inda a kokarin sa na neman kubucewa ya ci karo da wata mota yayin da take tsala gudu da nan take ta murkushe shi har lahira.
Majiyar rahoton ta bayyana cewa, laifin da wannan dan kabu-kabu ya aikata shine rashin bayar da cin hanci na N100 da Jami'in dan sandan Sajen Magaji tare da abokan sa na aikin su ka bukata.
Sai dai hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa, Motar ta talitse Marigayi Samuel ne yayin da yake kokarin arcewa sakamakon jami'an da suka hange sa yana zukar tabar wiwi daura da ofishin su.
Wani mai kare hakkin dan Adam, Dede Uzor, ya yi tir gami da Allah wadai dangane da afkuwar wannan lamari, inda yake kira ga kwamishinan 'yan sanda na Jihar, Garba Umar, akan ya tabbatar an gudanar da adalci cikin lamarin.
KARANTA KUMA: Zaben 2019: Jihar Kano ta Buhari ce - Ganduje
Uzor wanda shine shugaban kungiyar masu kare 'yancin bil Adama ta Najeriya ya bayyana cewa, akwai ire-iren wannan korafi da suke samu musamman daga 'yan kasuwa, masu ababen hawa da kuma mazauna wannan yanki dangane da matsi na jami'an 'yan sanda.
Shugaban wannan ofishin na 'yan sanda, SP Godson Ubani, ya bayyana cewa, wannan zargi da tuhuma na Uzor da Marigayi Samuel basu da tushe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng