Satar Man Fetur ta jefa wasu 'Yan Najeriya 3 da 'Yan Kasar Ghana 2 a Gidan Wakafi
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wata kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas ta jefa wasu mutane 3 'yan Kasar nan ta Najeriya da kuma wasu biyu 'yan Kasar Ghana a gidan Kaso bisa laifin satar wani adadi mai yawa na man fetur.
Shafin jaridar Premium Times ya bayar da sunayen wannan mutane da ake zargi kamar haka; Shadrack Eneogwu, Ojo Christopher, Atolagbe Hakeem, Daniel Oluwatobi, John Kwane Amissah da kuma Jonathan Kumah Tetteh.
Rahotanni sun bayyana cewa, an gurfanar da wannan Mutane tare da taragon su da kuma wasu kamfonin biyu na Macchalis International Limited da Ayoknok Ventures Limited a gaban Alkaliyar Kotun, Hadiza Rabiu Shagari.
Legit.ng ta fahimci cewa, daya daga wannan mutane da ake zargi Shadrack Eneogwu, ya dannan layar bata a yayin da hukumar EFCC take ci gaba da neman sa.
KARANTA KUMA: Wani Farfesa ya gamu da Ajali cikin Ofishin sa a wata Jami'ar Jihar Bayelsa
Wannan laifuka kamar yadda Idris Muhammad, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun, sun sabawa sashe na 3 da na 1 cikin dokokin da gwamnatin tarayya ta gindaya tun a shekarar 2004 da ta gabata.
Lauyoyin masu kare wadanda ake zargi, Olalekan Ojo da Dorothy Bassey, sun nemi kotu da ba su dama ta roƙon bayar da belin su.
Alkaliyar Kotun Ms Rabi'u Shagari, ta bayar da umarnin tsare wannan mutane a gidan Kaso na Ikoyi yayin da daga sauraron neman roƙon bayar da belin su zuwa ranar 26 ga watan Yuni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng