Ko da naka, ka so na kwarai: Wani tsohon 'dan takaran shugaban kasa ya sallamawa Buhari
- Mutane da dama na kara nuna goyon bayansu ga shugaba Muhammadu Buhari gabanin zaben 2019
- Wani tsohon dan takarar shugabancin kasa, Rafiu Salau ya ce babu wanda yafi dacewa ya jagoranci Najeriya fiye da Buhari
- Salau ya fito takaran shugabancin kasa a 2015 karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) amma daga baya ya janye don marawa Buhari baya
Rafiu Salau, dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) a zaben 2015 ya jadada goyon bayansa ga tazarcen shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce babu wanda yafi dacewa ya jagoranci Najeriya fiye da Buhari.
Idan ba'a manta ba Salau ya janye daga takarar shugabancin kasar a shekarar 2015 ne inda ya amince da goyon bayan dan takaran jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram
Legit.ng ta gano cewa Salau ya yi imanin cewa shugaba Muhammadu Buhari ne zai lashe zaben 2019 da kuri'u masu yawa.
A cewar tsohon dan takarar shugabancin kasar, Buhari ne mutum daya tilo da zai iya jagorancin Najeriya don rike matsayinta a nahiyar Afrika da duniya baki daya.
Ya ce: "Zan cigaba da goyon bayan sa saboda na san daga karshe, al'ummar Najeriya za suyi murmushi bayan sun fahimci cewa duka abinda ya aikata ya yi ne don cigaban kasa.
"Yana da kyau yan Najeriya su sani cewa Najeriya za ta samu cigaba sosai ne idan aka bari shugaba Buhari ya karasa sauran shekaru hudu a matsayinsa na shugaban kasa saboda Allah ne ya yiwa Najeriya baiwa da Buhari."
A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban cibiyar yaki da rashawa da shugabanci na gari (CACOL), Debo Adeniran ya bayyana cewa shugaba Buhari ne yafi dacewa ya cigaba da jan ragamar mulkin Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng