Ruwa, rana da iska: Yadda yanayin garuruwan musulmin Najeriya 15 za su kasance yau Sallah
- Hukumar dake da alhakin hasashen yanayi a Najeriya ta ce za'a yi hazo a jahohin tsakiyar Najeriya
- Haka hukumar hasaso za'a yi mamakon ruwa a garuruwan Abuja, Minna da Jos
- Haka zalika dai ta yi hasashen ruwan a jahohi da dama a kuddancin Najeriya
Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da yanayin kasa watau Nigerian Meteorological Agency (NiMet) ta saki rahoton hasashen yadda yanayin wasu garuruwan musulmin Najeriya za su kasance yau Juma'a 15 ga watan Yuni, kuma ranar Sallah.
KU KARANTA: An ga wata a Najeriya inji Sarkin musulmi
Rahoton hasashen dai ya ce za'a iya yin ruwa sosai a garuruwan Abuja, Minna, Jos da kuma Lakwaja da rana zuwa marecen yau din.
Haka ma dai ruwan za'a maka a garuruwan Akure, Osogbo, Ado-Ekiti, Legas, Enugu, Owerri, Abakalki, Fatakwal, Kalaba da Eket yai din.
Haka dai ana sa ran a sheka ruwa a garuruwan arewacin Najeriya kamar Nguru, Potiskum, Dutse da Katsina da safiyar yau kamar dai yadda hasashen ya nuna.
Su ma garuruwan Yelwa, Sokoto da Gusau ana sa ran ayi masu ruwa amma da yamma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng