Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe

Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe

Mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Yobe Alhaji IBrahim Gaidam, ya bayar da lamunin sa na sanya dokar takunkumi na zirga-zirga da ababen hawa har na tsawon sa'o'i 12 a fadin jihar da kewaye.

Kamar yadda kakakin gwamnatin jihar Mallam Abdullahi Bego ya bayyana, dokar ta takukumi za ta fara aiki daga 10.00 na daren yau jajiberin Sallah zuwa 10.00 na safiyar gobe ta Juma'a da ta yi daidai da ranar Idi na karamar Sallah.

A cikin sanarwar da kakakin gwamnatin jihar ya bayyana, wannan takunkumi zai hadar har da zirga-zirga da ababen hawa zuwa Mallatai na Idi.

Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe
Gwamnati ta sanya takunkumin zirga-zirga da ababen hawa na tsawon sa'o'i 12 a Jihar Yobe

Sai dai Legit.ng ta fahimci cewa, wannan doka ba ta shafi jami'an tsaro da kuma masu bukata ta gaggawa.

KARANTA KUMA: Kamfanonin Jiragen sama na Najeriya sun sayar da Tikiti na N505bn a shekarar 2017

Mallam Bego ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne domin tabbatar da an gudanar da Bikin Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da wata tangarda ba.

A sanadiyar haka gwamnan jihar ya nemi al'ummar jihar akan kiyaye ka'idojin wannan doka domin zaman Lafiya da hausawa kan ce ya fi zama dan Sarki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel