Kyautar kudi har N12m ga wanda ya kirkiro yadda ake gwajin malaria ba tare da huda jiki ba

Kyautar kudi har N12m ga wanda ya kirkiro yadda ake gwajin malaria ba tare da huda jiki ba

- Cutar maleriya wadda sauro ke yada wa tafi kowacce cuta kisa a tarihin dan Adam

- Maleriya tafi yaduwa a kasashen Afirka, kudu da hamada inda kazanta kan tara sauro

- A baya sai an huda an debi jini ake iya gano cutar kafin magance ta

Kyautar kudi har N12m ga wanda ya kirkiro yadda ake gwajin malaria ba tare da huda jiki ba
Kyautar kudi har N12m ga wanda ya kirkiro yadda ake gwajin malaria ba tare da huda jiki ba

Wani saurayi, dan asalin kasar Uganda dake gabashin Afirka, ya lashe kyautar akalla naira miliyan 12 in aka juya zuwa dala, saboda fasaharsa ta kirkiro maganin cutar malariya wadda akan iya gano wa ba tare da an huda fata ba.

Brian Gitta, dan shekaru 24, ya lashe kyautar ne ta Royal Academy of Engineering's Africa Prize a Ingila, wadda ta bashi dala $33,000 domin ya samar da takanoloji da babu irinsa a baya ta hanyar fasaha.

Injin da ya kero, yana haska dan yatsa ne kawai, maimakon a kwashi jini a auna a leka kafin gano cutar don magance ta.kafin tayi kisa.

DUBA WANNAN: Farashin kayyayyaki sun fara sauka

Yayi kokarin ganowa ne domin shi jininsa baya nuna cutar koda ta kama shi, sai kawai ya kirkiri na'urar wadda zata kalli yadda gudanar jini take daga dan yatsa.

Idan aka ga fararen 'ya'yan jini, wadanda suke yakar cutar a warwatse, akan gane haka suke idan maleriyar ta shigi mutum.

An fara samar da hasken har a wayar salula a matsayin App.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng