Ba ruwan su da ganin wata, wasu musulmin Najeriya sun sha bikin sallah a yau

Ba ruwan su da ganin wata, wasu musulmin Najeriya sun sha bikin sallah a yau

- Babban limamin Ibadan, Sheikh AbdulGaniyu ya janyo cece-kuce tsakanin musulmi bayan ya jagoranci sallar Eid-el-fitr a yau Alhamis 14 ga watan Yuni

- An ruwaito cewa ya jagorancin sallah idi tare da wasu manyan mutane a filin idi na Agodi da ke Ibadan

- Musulmi dai basu yin sallar Idi har sai an ga jaririyar watan shawwal kuma a halin yanzu ba'a ga watan ba

Mutane da dama suna da suka ga babban limanin garin Ibadan, Sheikh AbdulGaniyu Agbotomokekere saboda jagorantar sallar idi a yau Alhamis 14 ga watan Yunin 2018.

Idan ba'a manta ba dai gwamnatin tarayya da sanar da cewa ranar Juma'a za ta kasance hutun sallah ne saboda ana sa ran kammala azumin watan Ramadan a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ba ruwan su da ganin wata, wasu musulmin Najeriya sun sha bikin sallaha a yau
Ba ruwan su da ganin wata, wasu musulmin Najeriya sun sha bikin sallaha a yau

Legit.ng ta gano cewa babban limamin ya jogorancin sallar idi a Agodi kuma wasu fittatun mutane da dama a garin sun hallarci sallar idin.

KU KARANTA: Ba zan iya tabbatar da nagartar hadiman Buhari ba - Keyamo

A cewar wasu musulmi, abinda babban limamin ya aikata ya sabawa umurnin kwamitin koli na harkokin musulunci na Najeriya.

Sai dai har yanzu, Sultan Sa'ad Abubakar III wanda shine ke jagorancin kwamitin kolin ta harkokin addinin musulunci bai ce komai game da wannan lamarin ba.

Mabiya addinin musulunci sun bayyana cewa jaririyar watan Shawwal din ne ke nuna karshen azumin watan Ramadan da aka kwashe kwanaki 29 ana yi.

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnati tarayya ta ayyana cewa ranar Juma'a 15 ga watan Yunin 2018 a matsayin ranar hutu saboda shagulgulan sallah karama.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ne ya bayar da sanarwan a ranar Litinin, 11 ga watan Yunin 2018

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: