Fashin Offa: Hukumar 'Yan sanda ta sake cafke wasu da ake zargi a jihohin Kogi da Oyo tare da Muggan Makamai
Da sanadin jagorancin Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda, Abba Kyari, Hukumar ta samu nasarar cafke wasu miyagu da ake zargin su da yin fashi da makamin da ya afku a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata a garin Offa.
Kamar yadda shafin Jaridar The Punch ya bayyana hukumar 'yan sanda ta sake cimma nasarar cafke wasu adadin mutane da ake zargin su da ta'addancin nan na jihar Kwara da ya salwantar da rayuwar jami'an 'yan sanda 9 tare da wasu mutane 33 a garin na Offa.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne hukumar ta sake cafke wasu da ake zargin hannun su cikin fashi da Makamin a jihohin Kwara, Oyo da kuma jihar Kogi.
Majiyar rahoton ta bayyana cewa a halin yanzu wannan 'yan ta'adda na taimakawa jami'an tsaro da rahotanni da za su kai ga cafke sauran abokan ta'addanci su.
KARANTA KUMA: Kasar Spain ta kori Kocin ta a Jajiberin Gasar cin Kofin Duniya
Legit.ng ta fahimci cewa, duk da dai Majiyar ba ta bayyana adadin 'yan ta'addan da aka cafke ba, ta bayar da tabbacin Makaman bindigu biyu kirar AK 47 da hukumar 'yan sanda ta samu nasarar cafkewa a hannun su.
A yayin haka kuma, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya barrantar da kansa daga duk wata dangantaka ko alaka tsakanin sa da wannan 'yan tadda da suka aikata fashi da makamin a wani banki dake garin Offa.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, fitaccen Lauyan na Najeriya Festus Keyamo, ya bayyana cewa akidar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta sauya al'adun siyasar kasar ne ita ce za ta tabbatar da nasarar sa a zaben 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng