Jerin sunayen tsoffin gwamnoni 23 da adadin kudaden da ake zargin sun wawura
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu na cigaba da farautan barayin gwamnati da ake zargi da wawure kudin kasa a lokacin da suke rike da kujerar mulki.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jajirce wajen ganin ta binciki wadannan mutane musamman ma tsoffin gwamnonin kasar.
A halin yanzu an samu wata mai shari’a wacce ta kafa tarihi, ta hanyar daure tsoffin gwamnoni biyu da aka samu da hannu dumu-dumu wajen sace kudaden jiharsu a lokacin da suke kan mulki.
Kamar dai yadda kuka sani akwai tsoffin gwamnoni da dama ake tuhuma da laifin aikata rashawa da rashin bin ka’idojin kashe dukiyar talakawa.
Don haka mukayi amfani da wannan dama wajen kawo maku jerin sunayen wadannan tsoffin gwamnoni su 23 da kuma adadin kudaden ake tuhumarsu da wawurewa.
KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani mutum bayan yayi yunkurin yiwa mai ciki fyade
Gas u kamar haka:
1. Saminu Turaki - N36bn
2. Murtala Nyako - N29bn
3. Danjuma Goje - N25bn
4. Timipre Sylva - N19.2bn
5. Abdullahi Adamu - N15bn
6. Attahiru Bafarawa - N15bn
7. Otunba Alao-Akala - N11.5bn
8. Ibrahim Shehu Shema - N11bn
9. Aliyu Akwe Doma - N8bn
10. Gbenga Daniel - N7bn
11. Chimaroke Nnamani - N5bn
12. Babangida Aliyu - N5bn (2 cases)
13. Rasheed Ladoja - N4.7bn
14. Orji Uzor Kalu - N3.2bn
15. Gabriel Suswan - N3.1bn
16. Ahmadu Umaru Fintiri - N2.9bn
17. Jolly Nyame - N1.64bn (an kammala shari'a)
18. Sule Lamido - N1.3bn
19. Joshua Dariye - N1.16bn (an kammala shari'a)
20. Ahmed Sani Yerima - N1bn
21. Ikedi Ohakim - N270m
22. James Bala Ngilari - N167m
23. Bukola Saraki - Bayyana kadarorin bogi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng