Duniya tayi zafi: Yadda wani dan Najeriya ya kashe Kansa, Uwargidarsa da Diyarsa

Duniya tayi zafi: Yadda wani dan Najeriya ya kashe Kansa, Uwargidarsa da Diyarsa

Wani dan Najeriya kwararre a fannin hade haden magunguna, Olasukanmi mai shekaru 41 ya yanke wa kansa mummunar hukunci, inda ya aikata ma kansa da iyalansa sabalikita ta hanyar bindige Matarsa, Bourk Esho da diyarsu Olivia, daga bisani ya dauki ransa da kansa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari mai tsananin muni ya faru ne a da misalin karfe 1 na daren Lahadin da ta gabata a gidansu dake Farmingdale Drive a garin Chicago na kasar Amurka, a wannan lokaci ne Yansanda suka garzaya gidan, suka tarar da gawarwakin mamatan.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna da aka yanke masa shekaru 14 a gidan Yari yace duk yan Najeriya barayi ne

Duniya tayi zafi: Yadda wani dan Najeriya ya kashe Kansa, Uwargidarsa da Diyarsa
Iyalan

Rahotanni sun nuna cewar Maigidan ya yi nufin kashe kansa ne, toh amma sai ya ga dacewar ya fara da Uwargidarsa Bourk mai shekaru 33 yar asalin kasar Kamaru da yarsu mai shekaru 7, sai dai babban dansu mai shekaru 13, da yar autansu mai shekaru 4 sun sha da kyar.

Babban dan nasu ya tsallake rijiya da baya ne a yayin da tsere da gudu waje bayan ya ji harbin bindiga da nufin ya je ya fada ma mahaifiyarsu, ashe bai san Uwartasa mahaifinsu ya bindige ba, dawowarsa gida keda wuya sai ya tarar da gawarsu kwance cikin jini.

Duniya tayi zafi: Yadda wani dan Najeriya ya kashe Kansa, Uwargidarsa da Diyarsa
Gidansu

Nan take yaron ya fashe da kuka yana kuwwa sakamakon rashin Uba, Uwa da kanwa da yayi, sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin dalilin tafka wannan danyen aiki da Olasukanmi ya yi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: