Alkalumma sun nuna farashi ya fara saukowa bayan tashin gwauron zabi a baya
- Kayan masarufi na saukowa bayan da a baya suka hau da farashi
- Wannan na nufin Najeriya ta shawo kan matsalar tattalin arzikinta
- Ya zuwa yanzu gwamnati ta dauki matakai da zasu gyara darajar Naira
Kudaden da ake siyan kayayyaki wanda cibiyar alkalumma ta kasa, watau National Bureau of Statistics ta saki ranar laraba ya nuna cewa tsadar kaya ta ragu da kashi 12.48 a cikin dari a watan Afirilu zuwa kashi 11.61 kashi 11.61 a cikin dari a watan Mayu.
A rahoton ta tace wannan ne wata na 16 a jere da farashin kayayyakin suke sauka.
Rahoton ya nuna cewa "farashin da masu siyan kayayyakin ya kai kashi, 11.61 cikin dari (a duk shekara) a Mayu, 2018. Wannan ya nuna raguwar tsadar kayan da kashi 0.87 a cikin dari kasa da wanda aka wassafa a watan Afirilu 2018 kuma ya nuna Karo na 16 da yake raguwa a jere."
DUBA WANNAN: Cikakkun bayanai kan yadda Dariye ya karke a kotu
Kayayyakin masarufi da na more rayuwa sunyi tashin gwauron zabi a 2015 da 2016, sai dai a 2017 abubuwa sun nuna daidaito.
A yanzu kuma kamar abubuwa sun kama hanyar warwarewa da ma saukowa yadda kowa zai iya saya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng