Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba

Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba

A yau Laraba ne Hukumar Sojin Ruwan Najeriya da ke Jihar Delta ta sanar da cewa ta lalata sama da matatun man fetur 1000 wanda aka gina su ba bisa ka'ida ba a yankunan Neja Delta.

A yayin da yake hira da manema labarai a Warri, Kwamandan NNS Delta, Commodore Ibrahim Dewu ya ce an lalata haramtattun matatun man fetur din ne a cikin kwanaki 29 da suka shude a wata simame da rundunar keyi.

Ya ce rundunarsa ta lalata haramtattun matatun man fetur a Otumara, Ogbegugu, Okpuku da Bennet inda su kayi amfani da na'ura ta musamman mai suna swamp buggies tare da motocin da ke iya shiga ruwa.

Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba
Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba

KU KARANTA: Abubuwan da muka tattauna jiya a taron da mu kayi da Buhari - Okorocha

"Mun fara amfani da motocci na musamman masu ratsa tabo 'swamp buggies' ne saboda basu lalata muhalli kuma sukan hana masu wannan mummunan sana'a sake kafa matatan man fetur din bayan mun lalata kayayakin aikinsu.

"A halin yanzu dai muna samun nasara sosai kuma ba za muyi kasa a gwuiwa ba har sai mun tabbatar dukkan masu aikata wannan sana'a sun dena," inji shi.

A baya, Sojin Ruwan Najeriya suna amfani da manyan bindigogi ne wajen lalata matatun man fetur din da ba bisa ka'ida ba.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa masu matatun man fetur din na bogi sun bullo da wata sabuwar dabarar hana sojojin gudanar da ayyukansu.

"Masu matatun man fetur na bogi a Bennett Island sukan zagaye matatun man fetur din da wuta don su hana mu shiga wurin da suke barnar.

"Sai dai duk da hakan, muna gano hanyoyin da zamu ratsa cikin matatun man fetur din kuma mu lalata kayayakinsu duk da hayaki da ruwa.

"Tunda muka fara amfani da sabuwar fasahar swamp buggies, masu aikata wannan laifin sun shiga uku," inji Kwamandan.

Hakan yasa wasu daga cikinsu ke kiraye-kirayen tsige kwamandan, sojin hadin gwuiwa (JTF) ta rundunar "Operation Delta Safe," Rear Adm. Suleiman Apochi. Kiraye-kirayen tsige shi ba zai sa mu dena aikinmu ba.

Daga karshe ya gargadi masu irin wannan mummunar sana'ar su dena in kuma ba haka ba su fuskanci fushin hukuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel