Za a sake Karrama Wasu 'Yan Najeriya - Boss Mustapha

Za a sake Karrama Wasu 'Yan Najeriya - Boss Mustapha

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta sake karrama wasu fitattun 'yan Najeriya a nan gaba.

Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata yayin gabatar da jawaban sa na lale maraba yayin bikin karamcin jaruman Dimokuradiyya da kuma kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokuradiyyar Kasar nan.

A safiyar ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Marigayi Cif MKO Abiola da mafi kololuwar mukami na GCFR watau mukamin Shugabannin Kasa na yanzu ko wanda suka shude.

Shugaba Buhari yayin bikin karrama Marigayi MKO Abiola
Shugaba Buhari yayin bikin karrama Marigayi MKO Abiola

A yayin da aka karrama Abiola duk da kasancewar baya doron kasa, shugaba Buhari ya karrama abokin takarar sa, Babagana Kingibe da mukamin GCON (Grand Commander of the Order of the Niger).

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya bayar da sanarwa kaddamar da 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar Dimokuradiyyar Kasar nan sabanin yadda aka saba gudanar da murnar ta a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara.

KARANTA KUMA: Mutane 40 sun shiga Hannu da Laifin yada Jita-Jita a Dandalin Sada Zumunta

Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da wannan biki na karramaci a fadar shugaban kasa domin karrama gwaraza da jaruman da suka assasa Dimokuradiyya cikin Siyasar Kasar nan.

Cikin jawaban nasa, Sakataren gwamnatin ya bayar da sanarwar cewa akwai wasu fitattun mutane na daban da shugaba Buhari zai sake karramawa a nan gaba sakamakon gudunmuwa da rawar da suka taka wajen assasa Dimokuradiyya cikin gwamnatin Kasar nan.

Yake cewa, gwamnatin za ta fayyace sunayen wadanda za ta karrama cikin wasu 'yan lokuta a nan gaba domin yabawa gudunmuwa ta saudaukar da kai ga Kasar nan ta Najeriya tare da dabbaka Dimokuradiyya cikin tsarin gwamnatin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng