June 12: Ba zamu lamunci soke zabe a Najeriya ba, Dan ba kara – Buhari

June 12: Ba zamu lamunci soke zabe a Najeriya ba, Dan ba kara – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a yanzu an wuce lokacin da za’a soke zabe a Najeriya kamar yadda aka yi a zaben shekarar 1993, don haka yan Najeriya ba zasu sake lamuntar haka ba a nan gaba, inji rahoton Daily Trust.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 12 ga watan Yuni a yayin bikin tunawa tare da karramayan gwagwarmayan zaben June 12 na shekarar 1993 da ya gudana a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: June 12: Mu Yarbawa za muyi ma Buhari ruwan kuri’u – Inji Bola Tinubu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin taron Buhari ya karrama marigayi MKO Abiola, don takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP na wannan zabe, kuma wanda ake ganin shine kan gaba wajen lashe zaben, da lamba girmamawa ta GCFR.

Haka zalika Buhari ya karrama mataimakin Abiola a wannan zabe, Babagana Kingibe da marigayi tsogon lauya dan gwagwarmaya, Gani Fawehinmi da lamgar girma ta GCON, sai dai shugaba Buhari yace yayi hakan ne da nufin kwantar da hankulan yan kasa.

Daga karshe Buhari ya nemi gafarar iyalan Abiola, yan uwa da abokan arziki bisa cin amanar da gwamnatin mulkin Soja ta yi ma Abiola, da ma sauran wadanda suka fafata da wadanda suka mutu a yayin gwagwarmayar siyasar June 12.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng