June 12: Sanata Shehu Sani ya bayyana babban aminin Abiola a yankin Arewa

June 12: Sanata Shehu Sani ya bayyana babban aminin Abiola a yankin Arewa

Wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, kuma shugaban kwamitin bada rance na majalisar, Sanata Shehu Sani ya bayyana babban shakikin aminin tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 1993, marigayi Moshood Kashimawo Abiola, a yankin Arewacin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Shehu ya fasa kwan ne a shafinsa na Tuwita, inda yace Abiola da kansa ya bayyana masa cewar mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ne amininsa na kud da kud a gaba daya Arewa.

KU KARANTA: Kudin tsafi: Yadda wasu mutane 4 suka hallaka abokinsu suka guntule zuciyarsa

June 12: Sanata Shehu Sani ya bayyana babban aminin Abiola a yankin Arewa
Abiola da Sarki

Sanatan yace Abiola ya fada masa a shekaru aru aru da suka gabata cewa Sarkin ne kadai amininsa da yake iya tattauna sirrinsa da shi a duk cikin abokansa dake Arewa, ya kara da cewa alakarsu ba ta siyasa bace.

June 12: Sanata Shehu Sani ya bayyana babban aminin Abiola a yankin Arewa
Shehu, Abiola da Gambo Sawaba

“A duk Arewa MKO Abioa ba shi da abokin da ya wuce Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, kuma alakarsu ba ta siyasa bace, abotan gaskiya ce, Abiola da kansa ya fada mini haka.” Inji Shehu Sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng