Jarumin soja: Hotunan yadda wani soja ya diro daga samaniya domin sanyawa budurwar sa zoben kauna (Bidiyo)

Jarumin soja: Hotunan yadda wani soja ya diro daga samaniya domin sanyawa budurwar sa zoben kauna (Bidiyo)

Ko shakka babu soyayya kan sa mutum ya dimauci wani lokacin ma hadda zaucewa musamman ma wajen aikata wasu bakin abubuwa duk domin ya burge abar kaunar sa.

Haka zalika su ma dai sojoji duk da ba kasafai ake alakanta su da soyayyaba suna suna dan taba dai-dai iya tasu.

Jarumin soja: Hotunan yadda wani soja ya diro daga samani domin sanyawa budurwar sa zoben kauna (Bidiyo)
Jarumin soja: Hotunan yadda wani soja ya diro daga samani domin sanyawa budurwar sa zoben kauna (Bidiyo)

KU KARANTA: Kishi ya sa wani matashi yayi wa budurwar sa yankan rago

A wannan labarin da muka samu, wani sojon Najeriya ne mai suna Mordecai Danladi ya yi kukan kura ya diro tare da lemar jirgi daga kololuwar sama domin kawai ya sanya wa masoyoyar sa zoben kauna.

Ga faifan bidiyon nan a kasa:

Ita kuwa budurwar mai suna Anna Bako, ta nuna matukar jin dadin ta ne game da yadda masoyin nata ya nuna jarumta wajen tabbatar da kaunar sa a garet

Dukkan lamarin dai kamar yadda muka samu ya faru ne a kan idanun abokan aikin sun sojoji a cikin dokar daji.

Haka zalika mun samu cewa Anna Bako ta amince da soyayyar jarumin sojan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel