Abiola: Manyan kasar nan ne suka yi tuggun hana shi mulki a 1993 - Aso Rock

Abiola: Manyan kasar nan ne suka yi tuggun hana shi mulki a 1993 - Aso Rock

- Malam Garba yace manyan kasar nan ne suka hada kai suka hana IBB ya bashi mulki

- An sa rai Abiola ne ya lashe zabukan 1993

- Sa tuni sai a 2001 zai gama mulkinsa bayan kayarda Bashir Tofa

Abiola: Manyan kasar nan ne suka yi tuggun hana shi mulki a 1993 - Aso Rock
Abiola: Manyan kasar nan ne suka yi tuggun hana shi mulki a 1993 - Aso Rock

Malam Garba Shehu, hadimin shugaba Buhari kan harkokin yada labaru, ya bayyana yadda aka shirya tuggun da ta kawo rikita-rikitar siyasa da ta kai kasar nan dab da rugujewa, inda yace wasu manyan kasar nan basu ji dadin yadda shugaba Buhari ya kyautata alheri don gyara sharrin baya ba.

A cewar Malam Garba Shehu, ba wai kawai sojoji ne suka murda zaben ba, a'a, akwai 'yan siyasa, masu mulki, bangarorin sharia, da wasu 'yan siyasar da suka sanya hannu, kuma suka bada gudummawar kayar da dorarriyar dimokuradiyyar da ta zo dab da kamawa a 1993.

Bayan an hana fadin sakamakon zaben dai, an mika wa gwamnatin rikon kwarya sannan aka mika wa sojoji mulkin ta bayan gida, wadanda su kuma suka garkame Abiola har ya rasa ransa.

DUBA WANNAN: An bada kwangilar gyaran Ogoni

A kokarin karrama Abiola da abokan tafiyarsa dai, shugaba Buhari yayi kokarin farantawa wasu bangarori na Najeriya rai, sannan kuma ya bakantawa wasu, musamman manyan kasar nan.

Malam Garba shehu ya kara da cewa, da wuya kaga manyan kasar nan sun hada kai kan wani abin alheri, sai dai fa sharri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel