An kori jami’an ‘yan sanda 8 daga aiki a jihar Legas, karanta laifukan da suka aikata
A kalla jami’an ‘yan sanda 8 aka kora daga bakin aiki daga watan Janairu zuwa yanzu a jihar Legas kamar yadda hukumar ta ‘yan sanda ta sanar a jihar.
Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ne ya sanar da wadannan alkaluma ga manema labarai, jiya, Lahadi.
Oti ya kara da cewa an ragewa wasu jami’ai 4 mukami yayin da aka yiwa wasu jami’ai 28 kashedi mai tsanani.
Da yake bayyana dalilan sallamar ‘yan sandan daga aiki, Oti, ya ce uku daga cikin jami’an an sallame su ne saboda fesawa wani mutum, Mista Ademuwagun Temotope Solomon, barkonon tsohuwa a garin Festac. Lamarin ya haddasawa Ademuwagun kamuwa da cutar asma.
Ya kara da cewar, an gurfanar da jami’an; Saja biyu da Insfekta daya, kuma an same su da laifi.
Kakakin ya kara da cewa, dukkan ‘yan sandan an gurfanar da su domin tabbatar da an yi masu adalci kafin ta kai ga an kore su daga aiki ko kuma yi masu hukunci a kan saba dokar aiki.
DUBA WANNAN: Diyar marigayi Abiola ta farkewa Obasanjo laya, tayi masa wankin babban bargo
Bayan jami’ai 8 da aka kora, Oti, ya ce an ragewa wasu jami’ai 4 mukami yayin da wasu 28 aka yi masu kashedi mai tsanani sannan wasu jami’ai 3 na fuskantar horo mai tsanani.
Horon, a cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Edgal Imohim, tab akin Oti y ace an yi shi ne domin jami’an su gane kuskuren su kuma su gyara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng