Fallasa: Diyar marigayi Abiola ta farkewa Obsanjo laya, tayi masa wankin babban bargo
Tudun Abiola, diyar marigayi MKO Abiola ta bayyana cewar tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo bai ci zaben shekarar 1999 ba a Najeriya tare da bayyana cewar an dora shi ne a kan mulki kawai domin a kwantar da hankalin Yarabawa a kan abinda aka yiwa mahaifin ta.
Tudun ta kara da cewar, sojoji ne suka dasa Obasanjo a kan mulki domin ragewa ‘yan kabilar Yoruba radadin soke zaben Abiola na shekarar 1993.
“An dora Obasanjo ne kawai a kan mulki, ba zaben sa aka yi ba. Ba a yi zabe a shekarar 1999 ba, kawai an yi rantsuwa ne,” Tudun ta shaidawa gidan Talabijin na Channels.
Tudun na wadannan kalamai ne a matsayin martini ga karramawar da gwamnatin shugaba Buhari ta yiwa mahaifinta ta hanyar bas hi lambar girma ta GCFR da kuma mayar da 12 ga watan Yuni ranar dimokradiyya ta kasa.
DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wani mutum ya bar motar sa ta alfarma a tsakiyar titi tare da zundumawa cikin teku a Legas
Da take magana a kan karramawar, lauya Tudun, ta ce iyalin marigayi Abiola sun yi matukar farinciki da wannan girma da gwamnati ta bawa mahaifin su.
“Zai yi wuya ya mutun ta siyasa domin ba zabar sa aka yi ba. Obasanjo da mahaifina basa jituwa kuma haka ya cigaba da nunawa iyalan sa halin ko-in-kula, hakan ya saka ba zai karrama mahaifin mu a matsayin gwarzon siyasa ba,” a cewar Tudun.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng