Mata masu yoyon fitsari sun samu tagomashi daga Sarki Muhammadu Sunusi II (Hotuna)
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya yi kabakin alheri kan wasu mata dake dauke da lalurar yoyon fitsari dake jihar Kano, inda ya yi musu rabon kayan Sallah da kudin dinki, inji rahoton jaridar Rariya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mai Martaba Sarki ya baiwa matan nan wannan kayan alheri ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuni a yayin wata ziyara da ya kai mausu, tare da Diyarsa Yusrah.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka kasar Moroko, an masa tarbar girma
Su dai wadannan mata suna zaman jinya ne a cibiyar kula da masu cutar yoyon fitsarin da aka fi sani da suna ‘VVF’ a turance, dake unguwar Kwalli na jihar Kano.
Irin wannan aiki alheri ba sabon abu bane a wajen kanawa, inda ko a farkon cikin watan Azumin nan sai da jarumar fina finan Kannywood, Hadiza Gabon ta yi rabon kayan Sallah ga wasu mabarata gajiyayyu, haka zalika ta raba kayan abinci ga mabukata.
Shi ma fitaccen dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya yi irin wannan rabon kayan alheri ga mabukata da dama inda ya raba musu buhunan shinkafa, man girki, da dai sauran kayayyakin abinci da kuma kudi naira dubu goma goma.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng