Ka mika kan ka kawai a bincike ka, ka daina raki – Wani gwamna ya shawarci Obasanjo

Ka mika kan ka kawai a bincike ka, ka daina raki – Wani gwamna ya shawarci Obasanjo

A karshen makon da ya gabat ne tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, tab akin mai watsa labarn sa, Kehinde Akinyemi, ya bayyana cewar gwamnatin shugaba Buhari na shirin daure shi har sai baba-ta-gani.

Kalaman na Obasanjo sun jawo barkewar cece-kuce a Najeriya. A yayin da wasu ke yiwa gwamnati kashedi a kan taba Obasanjo, wasu kuwa murna suke da san barka tare da bawa gwamnati karfin gwuiwar Obasanjo.

Ka mika kan ka kawai a bincike ka, ka daina raki – Wani gwamna ya shawarci Obasanjo
Obasanjo da Fayose

A martanin gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewar Obasanjo ya mika kan sa domin a bincike shi, ya daina mita da korafi. Kazalika Fayose ya tambayi Obasanjo mai yake tsoro idan har yana da gaskiya tare da shawartar sa a kan kada ya jawo kowa cikin matsalar sa ko kuma yin kokarin alakanta abin da kabilar Yoruba.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Hukmar 'yan sanda ta kara gano wata alaka mai karfi tsakanin 'yan fashin Offa da Saraki

Obasanjo ya sha nuna mana shi jarumin soja ne da baya tsoron komai, a saboda haka shawara tag are shine kawai ya mika kan sa a bincike shi,” a cewar Fayose.

Dangantaka ta fara tsami ne tsakanin shugabannin biyu bayan wata wasika da Obasanjo ya aikewa Buhari, inda yake shawartar sa da ya hakura da batun tsayawa takara a zaben 2019. A nasa bangaren, shugaba Buhari ya zargi Obasanjo da barnatar kimanin dala biliyan $16 na wutar lantarki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel