Sanusi Lamido Sanusi: Mala'ika ne kawai za iya bashi shugabancin NNPC bai ci amana ba
Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu yace, harkar tallafin matatar man fetur ta kasa ya lalace, inda ya kai matsayin da babu wani dan Najeriya da za'a iya bashi amanar shugabancin wurin ba tare da yaci amana ba
Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu yace, harkar tallafin matatar man fetur ta kasa ya lalace, inda ya kai matsayin da babu wani dan Najeriya da za'a iya bashi amanar shugabancin wurin ba tare da yaci amana ba.
Sarki Sanusin yayi wannan batun ne a wata hira da yayi da manema labarai a wurin bikin murnar cikar sa shekaru 4 akan karagar mulki.
DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Shugaba Buhari ya saka hannu a wasu sabbin dokoki da zasu tayar da hankalin manyan kasar nan
An dakatar da Mai Martaba Sarki Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya a lokacin tsohon Shugaba kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2014, bayan da ya zargi shugabannin ma'aikatar man fetur din na wancan lokacin da wawushe dalar Amurka biliyan 20.
Yayi korafi akan rashin gaskiya na manyan masana'an tun mai na kasar nan wanda hakan ya biyo bayan rashin biyan tallafin man fetur din.
Da aka tambaye shi ko ya gamsu da yanda ake tafiyar da matatar karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sarkin yace babu wani abu ko guda daya canja akan yanda gwamnatin baya ta tafiyar da wurin, don haka babu wani canji da aka samu.
Sarkin yace, "Banga wata doka da aka sa don kawo canji a wurin ba. yana da matukar muhimmanci a saka dokoki da zasu kawo canje-canje a wannan ma'aikata."
Ya kara jaddada bukatar cire tallafin man fetur, Sarkin yace matsalolin ma'aikatar yafi karfin a canja shugabanni kawai, akwai muhimman canje - canje da ya kamata a gabatar domin kawo cigaba a wurin.
A karshe Sarkin ya kara da cewa, "Bawai mutanen da ke matatar bane amma maganar wai ace ana bukatar mutum mai gaskiya da rikon amana, sai dai ko idan mala'ika za a kawo wurin, domin kuwa shi kadai ne zai iya rike wurin ba tare da yaci amanar al'ummar kasa ba."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng