Wata 'yar sanda ta fadi dalilin da ya sa basu son auren fararen hula

Wata 'yar sanda ta fadi dalilin da ya sa basu son auren fararen hula

- Wata jami'ar Yan sanda, Tomilola Adekunle, ta bayyana bacin ranta kan yadda wasu mutane ke tsangwamar jami'an hukumar

- Ta bayyana cewa wasu mazajen da tayi soyaya da su a baya sun fada mata ba za su iya auran yar sanda ba saboda ba su yiwa maza da'a da biyaya

- Ta ce a halin yanzu tana soyaya da jami'in dan sanda ne saboda ta lura fararen hulan kawai so suke su yaudare su

Wata jami'ar Yan sanda, Tomilola Adekunle ta bayyana wa al'umma wasu daga cikin maganganu marasa kyau da mutane kan fadi a kan aikin dan sanda.

A wata hira da tayi da jaridar Punch, Tsaleliyar budurwar mai tatausan murya ta bayyana yadda iyayen ta suka so ta zama likita amma ta zama jami'ar Yan sanda bayan ganin yadda kanwar mahaifiyarta jami'ar yar sanda ke burgeta.

Legit.ng ta tattaro yadda Adekunle ke tunawa da yadda kanwar mahaifiyarta ke kasancewa cikin tsafta a kowanne lokacin kuma hakan yasa ta dau alwashin zama yar sanda idan ta girma.

KU KARANTA: Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

Ta ce: "Duk lokacin da na farka da safe naga kanwar mahaifiyata tana shirin zuwa aiki, na kan ayyana a zuciyata cewa tabbas sai na zama yar sanda; uniform dinta kullum cikin tsafta ya ke.

Wata kyakyawar 'yar sanda ta fadi dalilin da ya sa basu son auren fararen hula
Wata kyakyawar 'yar sanda ta fadi dalilin da ya sa basu son auren fararen hula

Sai dai, Adekunle ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda mutane da dama ke danganta aikin dan sanda da abubuwa marasa kyau.

Ta ce: "Kayan dan sanda ya kan kara wa mutum kima da daraja; duk lokacin da na saka kayan aiki na, mutane basu iya maganganun banza a kusa da ni musamman a cikin motar haya."

Ta kuma bayyana yadda soyayarta da wani saurayinta ya ruguje bayan ya gano cewa ita jami'ar yar sanda ne.

Kalamanta: "Lokacin da na ke jami'a, ina da wani saurayi dan ajin mu, mutane da dama suna sha'awar yadda soyayarmu ta ke .

"Ina yi masa girki, in wanke kayansa kuma in share masa gida duk mako. Bayan soyayar mu ta fara zurfa na fara yi masa tambayoyi akan rayursa sai dai baiyi na'am da hakan ba har ta kai ga ya koka kan yadda nake bincike game da rayuwarsa."

Hakan yasa ta gano akwai wasu abubuwa da saurayinta bai son ta sani game da shi. Hakan ya karya mata zuciya kuma dole suka rabu.

Ta ce dole ne a matsayinta na yar sanda ta tabbatar da cewa wanda take soyaya dashi ba mai aikata wasu laifuka bane a boye domin hakan na iya kawo mata cikas a aikinta.

Ta kuma bayyana yadda galibin mazajen da ta ke soyaya da su ke fada mata baza su iya aurar yar sanda ba saboda "sun fiye nuna isa kuma basu biyaya ga mazajen su."

Adekunle ta ce a yanzu tana soyaya ne da wani jami'in dan sanda dan uwanta kuma ta zabe shi ne saboda yadda fararen hula suka yaudare ta a baya. "Wasu mazan kawai suna son su cuce mu ne, wasu daga cikinsu mayaudara ne," inji ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel