Wata Sabuwa: Shugaba Buhari ya saka hannu a wasu sabbin dokoki da zasu tayar da hankalin manyan kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan dokar da zata tabbatar da duk lokacin da mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin shugaban kasa ko kuma mataimakin gwamna ya maye gurbin gwamnan, toh ba zai kara fitowa takarar samun kujerar ba fiye da sau daya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan dokar da zata tabbatar da duk lokacin da mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin shugaban kasa ko kuma mataimakin gwamna ya maye gurbin gwamnan, toh ba zai kara fitowa takarar samun kujerar ba fiye da sau daya.
DUBA WANNAN: Wani dutse mai aman wuta ya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 109
Babban mataimakin shugaban kasa na musamman akan harkokin majalisa, Ita Enang, ya bayyana hakan ga manema labarai yace, Maganar itace, tunda ka dau rantsuwar shugabancin da farko, zaka iya kara neman kujerar so daya ne kacal. Wannan shine manufar gyaran da shugaban kasar yake yi.
Sannan yace shugaba Buharin ya kuma kara saka hannu a wata doka ta ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa isasshen lokaci da zata yi zabe, cewa da an kara daga kwanaki bakwai zuwa ashirin da daya.
Enang ya kara da cewa shugaban kasar ya sa hannu akan dokar da ta ba majalisar jiha damar cin gashi kanta da kuma kotun jiha da masu shari'a.
Yace shugaban kasa yasa hannu akan dokar da ta danganci shirye shiryen zabe, rage lokutan da za'ayi zabe da kuma fitar da ranaku da za'ayi don tabbatar da cewa ba a shiga lokutan shari'a ba ko kuma ya kawo sagalewar shari'a.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng