Daliban wata jami'a sun rubuta jarrabawa akan Ramos da Salah
Rikicin da ya tilasta fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafar nan na Liverpool Mohammed Salah ficewa daga filin wasa yana kuka a mintuna 30 na karshe na wasan zakarun turai ya fito a wata jarrabawar nazarin ilimin sharia a wata makaranta a Damascus
Rikicin da ya tilasta fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafar nan na Liverpool Mohammed Salah ficewa daga filin wasa yana kuka a mintuna 30 na karshe na wasan zakarun turai ya fito a wata jarrabawar nazarin ilimin sharia a wata makaranta a Damascus.
DUBA WANNAN: Rashin kudi ne ya sanya ni halin dana ke ciki a yanzu
Hotunan takardar tambayoyin jarrabawar ta wasu daliban fannin sharia 'yan shekarar farko dake jami'ar Damascus ya mamaye ko ina a shafukan Facebook na kasar Syria.
A jikin takardar an tambayi daliban cewar: "Shin Sergio Ramos ya jiwa Mohammed Salah ciwo a wasan su na karshe na cin kofin zakarun Turai.
"A bisa yanda doka ta tanada baza a iya kama Ramos da laifin daya aikata ba, saboda wasu manyan sharudda guda hudu da suka shafi rikici a wasannin kwallon kafa. Lissafo wadannan sharudda."
"Wani yayi karin haske da cewar duk wani mai goyon bayan Barcelona zai yaga takardar jarrabawar sannan kuma ya fice daga dakin jarrabawar bayan yaji an ambaci Ramos."
Wasu kuma sun yabi Farfesan daya tsara tambayoyin musamman ma ga daliban domin kuwa zasu yi amfani da dokokin sharia domin gabatar da zahirin abinda ya faru.
Amsoshin tambaya mai sharudda guda hudu da Farfesan ya tambayi daliban sune:
1 - An gabatar da wasan ne a bisa doka.
2 - Dan wasan da yaji rauni, ya amince akan zai buga wasan.
3 - Dan wasan da yayi dalilin jin raunin, yana sane da dokoki da sharuddan wasan.
4 - Wannan shine ciwon da aka samu a lokacin wasan.
A kasa kuma hoton takardar jarrabawar ce tare da tambayoyin da Farfesan ya yiwa daliban daya bayan daya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng