Hankula sun tashi a garin Abuja yayin da yan Shia’a suka kona tutar Amurka da na Israila
Mabiya addinin Shia sun yi bikin babbaka tutocin kasashen Israila da Amurka a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuni, wanda hakan ya janyo tashin hankula a tsakanin mazauna Abujan, inji rahoton jaridar The Cables.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan shian sun bayyana cewa sun yi haka ne don nuna bacin ransu da kashe musu yan uwa Musulmai da ake yi a kasar Falasdin, inda suka tattaka daga babbab Masallacin Abuja zuwa shataletalen Julius Berger suna wake wake.
KU KARANTA: Wata daliba a jihar Sakkwato ta kashe jaririnta dan gaba da fatiha
Sai dai a yayin da suke zanga zangar tasu, jami’an Yansanda sun tattaru a sassa daban daban na babbanin birnin tarayyar don kare aukuwar wani rikici, da tabbatar da bin doka da oda.
‘Allah ya karya Amurka” “Allah ya ceci Falasdin” da kuma “A sako mana Zakzaky”, sune wasu daga cikin kalaman da suke furtawa a yayin da suke zanga zangar, inda daga bisani suka taru a kasar gadar Julius Berger, inda a nan ne suka kona tutocin.
Dama dai Yansanda sun sha karawa da yan shia a garin Abuja a lokuta daban daban, musamman a yayin zanga zangar neman a sako musu shugaban kasa Malam Ibrahim Zakzaky, wanda aka kama shi tun a shekarar 2015.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng