Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa babu gaira babu dalili

Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa babu gaira babu dalili

Hukuma ta damke wani mutum mai shekaru 37 da ake zargi da kashe mahaifiyarsa mai shekaru 65 ta hanyar daba mata wuka a gidansu da ke Oremeji a Legas.

An gano cewa wanda ake zargin, Nurudeen Bakare ya dade yana barazanar cewa sai ya halaka mahaifiyar sa.

KU KARANTA: Saraki da sauran 'yan majalisar dattawa ba su kauna ta - IGP Idris

Yayan wanda ake zargin, Sunday Tifase ne ya sanar da hukumar Yan sanda abinda da ya faru inda ya yi ikirarin cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuka ne ya daba wa mahaifiyarsa a ciki da wuya ba tare da wani dalili ba.

Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa babu gaira babu dalili
Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa babu gaira babu dalili

Kakakin hukumar Yan sanda na Legas, Chike Oti, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa za'a zurfafa bincike kan lamarin kana daga baya a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya don ayi masa shari'a.

A wata rahoton Legit.ng ta kawo muku labarin wata matashiya Munirat Bagana mai shekaru 19 da ake zargi da kashe jaririn da ta haifa a jihar Sakkwato.

Bagana, wadda yar asalin jihar Kebbi ne ta yi ikirarin cewa dama ba ta haifi jaririn da rai ba.

Duk da hakan Kakakin hukumar Yan sandan jihar, ASP Cordelia Nwawe ta ce za'a gurfanar da Bagana a gaban kotu bayan an gama bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164