Dubi irin kudaden da Amurka ta bawa Najeriya tallafi
Gwamnatin kasar Amurka ta bawa Najeriya tallafin miliyoyin daloli domin cigaba da agazawa al'ummar da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin arewa maso gabas
Da yake sanar da tallafin a jiya a babban birnin tarayya, Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Ambasada Stuart Symington, ya bayyana cewa tallafin da kasar Amurkan ta bayar na dala miliyan dari da biyu ($102), za ayi amfani dasu ne wurin agazawa wadanda suka fada cikin tashin hankalin Boko Haram a yankin arewa mso gabas, inda za'a samar musu wuraren zama, abinci, magunguna, da kuma tsaro a wuraren da abin ya shafa.
DUBA WANNAN: Trump ya hadawa musulmai shan ruwa a fadar White House
Tallafin yana daga cikin adadin kudin dala miliyan dari da goma sha biyu da kasar Amurka ta ware domin taimakon yankin tafkin Chadi.
Kasar ta Amurka tace tana fatan ace wannan tallafi data bayar ya zama sanadin samun karin aiki da kuma samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng