Trump ya hadawa musulmai shan ruwa a fadar White House

Trump ya hadawa musulmai shan ruwa a fadar White House

Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Amurka, da shugaban kasa ya kira shugabannin musulman duniya buda bakin azumi a fadar White House

Trump ya hadawa musulmai shan ruwa a fadar White House
Trump ya hadawa musulmai shan ruwa a fadar White House

Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Amurka, da shugaban kasa ya kira shugabannin musulman duniya buda bakin azumi a fadar White House. Shugaba Donald Trump wanda ya karbi mulki shekara daya da rabi da suka gabata, ya shirya walimar buda baki a fadar White House ta kasar Amurka.

DUBA WANNAN: FIFA: Najeriya ta sake fadowa kasa zuwa matsayi na 48 a duniya

Shugaban kasar na Amurka yayi watsi da al'adun fadar ta White House, inda ya aikawa shugabannin musulman duniya goron gayyata, domin su halarci buda bakin daya shirya domin su.

Fadar White House din taki bayyana sunayen wadanda suka samu halartar buda bakin, amma dai wasu majiyoyi daga fadar sun tabbatar da cewa a cikin wadanda suka samu damar halartar wannan walimar shan ruwa akwai wakilan kasashen Larabawa, irin su Saudiyya, Dubai, Jordan, Turkiyya, Masar, Tunusiya, Iraki, Bahrain, Qatar, Aljeriya, Libya da kuma kasar Morocco.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel