Uba, Uwa, Yara 3 da abokinsu 1 sun yi mutuwar ban mamaki kwana daya da tarewa a sabon gida

Uba, Uwa, Yara 3 da abokinsu 1 sun yi mutuwar ban mamaki kwana daya da tarewa a sabon gida

Rai bakon Duniya, inji Hausawa, wannan shine kwatankwacin abinda ya faru da wasu Iyali a jihar Ogun, inda Uba, Uwa da yayansu guda uku da kuma abokin yaran da ya kawo musu ziyara suka bakunci lahira a lokaci guda, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a tsohuwar titin Aiyepe dake garin Sagamu na jihar Ogun, kwana daya rak da tarewarsu a wani sabon gida da suka kama haya, inda ake zargin an yi ma gidan feshin guba ne.

KU KARANTA: Lokaci yayi da ya kamata ka gaggauta sakin Ibrahim Zakzaky – Gumi ga Buhari

Wani makwabcin mamatan, wanda da shi aka raka gawarsu zuwa babban asibitin Olabisi Onabanjo dake Sagamu, ya bayyana ma majiyarmu cewa wani wari suka jiyo daga gidan, wanda shi ya ja hankulansu zuwa gidan, inda suka tarar da gawarwakin mamatan.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun fara gudanar da binciken kwakwaf don gano musabbabin mutuwar iyalan.

Tun bayan samun labarin mutuwar mutanen dai daruruwan jama’a na ta tururuwa zuwa asibitin da ake mika gawarwakinsu don gane ma idanuwansu gaskiyar lamarin, tare da taya yan uwansu jimami da alhinin rashin da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel