Lokaci yayi da ya kamata ka gaggauta sakin Ibrahim Zakzaky – Gumi ga Buhari
Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta sakin shugaban yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, inji rahoton jaridar Rariya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gumi ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, yayin gabatar da Tafsirin Al’Qur’ni mai girma a Masallacin Sultan Bello, inda da fari sai nisanta kansa da akidar Shi’a, amma ya ga dacewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sako Zakzkay.
KU KARANTA: Wasu muhimman bayanai guda 7 game da Abiola, mutumin Buhari ya karrama
“Kowa a cikinku nan ba wani mai shakka, ko da masu shan 'Codeine' idan aka ce masa Ahmad Gumi Dan Shi'a zai yarda? Ba zai yarda ba. Saboda haka bana wani Shi'anci amma ina so in taimaki Gwamnati ne, don haka tunda Kotu tace a saki wannan mutumin (Zakzaky) ku sake shi." Inji shi.
Shehin Malamin ya cigaba da cewa "Idan ka sake mutum sai ya zama an sake shi gashi nan a wulakance, amma in ka rike shi to mabiyansa sai su yi ta kara daduwa, balle ma ga yunwa ga kisa, sai ace ah, to kun ga ai su ne Malaman Allah shi yasa aka kama su. Ina fada muku gaskiya, jama'arsa sai karuwa suke yi, amma a sake shi me zai iya?”
A wani labarin kuma, Gumi ya bukaci gwamnati ta daina cin zarafin tsofaffin gwamnoni musamman wadanda suka taimaki addinin Musulunci, inda ya yi kwatance da Ibrahim Shekarau, Ahmad Sani Yariman Bakura da Mukhtar Ramalan Yero.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng