Wasu muhimman bayanai guda 7 game da Abiola, mutumin Buhari ya karrama

Wasu muhimman bayanai guda 7 game da Abiola, mutumin Buhari ya karrama

Cif MKO Abiola, mutumin da ake masa zaton ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993, wanda ya gudana a ranar 12 ga watan Yuni, hamshakin dan kasuwa ne, kuma fitaccen dan siyasa, marubuci kuma dan babban gida daga kabilar Egba na Yarbawa.

Abiola ne mutumin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni, inda ya mayar da ranar da 12 ga Yuni, dake alanta ranar zaben da ya lashe a zamanin IBB, amma aka kwace zaben, a matsayin sabuwar ranar Dimukradiyya a Najeriya.

KU KARANTA: An yi ma Dansandan dake Tafsirin Qur’ani karin girma zuwa Kwamishinan Yansanda

Wasu muhimman bayanai guda 7 game da Abiola, mutumin Buhari ya karrama
Abiola

Sai dai Legit.ng ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da MKO Abiola:

1- An cire masa tsammani

Bayan haihuwarsa, mahaifinsa bai yi wani farin ciki ba, saboda duk dan da aka haifa masa namiji mutuwa yake yi, inda yaransa 22 duk sun mutu suna kanana, don haka bai yi zaton Abiola zai girma ba, a dalilin haka ya sanya masa suna ‘Kashimawo’ ma’ana bari mu gani. Har sai daya kai shekara 15 sa’annan aka rada masa suna Moshood.

2- Dan kasuwa kamar wani Sarki

Tun a lokacin dayake karami, Abiola ya nuna sha’awar yin kasuwanci, yana dan karamin yaro mai shekaru 9 ya fara harkar siyar da ice, inda yake zuwa daji da asubahi ya yo ice, sai ya dawo gida ya sayar kafin ya tafi makaranta, daga nan kuma har sai ya zama dan kasuwa da yafi shahara a nahiyar Afirka gaba daya.

3- Mawaki ne

A lokacin da ya kai shekaru 15, sai Abiola ya fara sha’awar harkar wake wake, dadaddiyar al’adar Yarbawa, inda ya fara zuwa tarukan suna da na aure yana yin wasa, ana bashi abinci, daga bisani ya shahara har ya aka fara biyansa da kudi, kudin da yake daukar nauyi iyayensa da karatunsa dasu.

4- Marubuci

A lokacin da ABiola ya fara tasawa a makarantar Sakandari ne ya shiga harkar rubuce rubuce, inda har aka zabe shi a matsayin jami’in tace rubutu na jaridar makaranatarsa, Sakandari Baptist dake garin Abekuta na jihar Ogun, a yayin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ke masa mataimaki, ya cigaba da rubutu har sai ya kafa kamfanin jarida, The Concord.

5- Jami’in Akanta

A shekarar 1956 ne Abiola ya fara aiki da bankin kasar Ingila, Barclays matsayin jami’in kula da kudi, wato Akanta, a garin Ibadan, bayan shekaru biyu ya samu cigaba zuwa hukumar kudi ya yankin Kudu maso yammacin kasar nan, daga nan kuma ya zarce kasar Scotland don karo ilimi, a inda ya samu shaidar digiri mafi daraja, First Class.

6- Gawurta a Kasuwanci

A zamanin rayuwarsa, Abiola ya fada harkokin kasuwanci daban daban, wanda ta kai gay a kafa kamfanoni da dama dake da dimbin ma’aikata a karkashinsu, daga ciki akwai: gonakai, shagunan littafai, gidan rediyo, gidan burodi, jaridar Concord, kamfanin jirgin sama, kamfanin harkar mai da iskar gas, kamfanin safurin jiragen ruwa, Bankin Habib, kungiyar kwallon kafa ta ABiola Babes, da sauransu.

7- Iyalan Abiola

Moshood Abiola ya auri mata dayawa a rayuwarsa, daga cikinsu akwai Simbiat Atinuke Shoaga, wanda ya aureta a shekarar 1960, Kudirat Olayinka Adeyemi a shekarar 1973, Adebisi Oshin a shekarar 1974, Doyin Abiola a shekarar 1981, Modube Abiola da kuma Remi Abiola, sa’annan yana da yara rututu.

Baya da sanar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimukradiyya, Buhari zai baiwa Abiola lambar yabo mafi girma a Najeriya duk da mutuwarsa, haka zalika zai baiwa mataimakinsa a wannan takara, Babagana Kingibe lambar yabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel