PDP ta sha kaye a hannun APC a zaben ciyaman na karamar hukumar Chikun a Kaduna

PDP ta sha kaye a hannun APC a zaben ciyaman na karamar hukumar Chikun a Kaduna

Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta yi nasarar lashe zaben shugaban karamar hukumar Chikun da aka sake yi a jihar Kaduna.

Baturen zaben karamar hukumar Chikun, Dakta Sani Mohammed, ne ya sanar da sakamakon zaben da aka maimaita jiya, Laraba, a sakatariyar hukumar da ke karamar hukumar Chikun.

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu kuri'u 52,660 yayin da ita kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 28,198, hakan ya nuna cewa jam'iyyar APC ta dara PDP da kuri'u 24,462.

Har ila yau: APC ta wancakalar da PDP a zaben maye gurbi na wata karamar hukuma a Kaduna
Har ila yau: APC ta wancakalar da PDP a zaben maye gurbi na wata karamar hukuma a Kaduna

Magoya bayan dan takarar APC da ya lashe zaben, Mista Maikai Adamu, wanda akafi sani da Adalo sun bayyana nasarar da ya samu a matsayin "nufi na Allah" yayin da wasu daga cikin magoya bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Mista Salasi Nuhu, suka shaidawa Politics Today cewar abinda ya basu mamaki shine yadda aka gudanar da zaben cikin lumana.

KU KARANTA: Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan an fadi sakamakon zaben, Ciyaman din APC a karamar hukumar Chikun ya bayyana farin cikinsa a kan amfani da sabuwar na'ura mai kwakwalwa wajen zaben, inda ya ce "ba mu taba tsamanin kananan jam'iyyu kamar APGA da makamantansu za su iya samun ko da kuri'a daya tak ba amma gashi sabuwar tsarin na yiwa kowa adalci."

An dai dage zaben karamar hukumar Chikun din ne bayan sanarwan da jami'an hukumar zabe ta jihar Kaduna (SIECOM) suka bayar a ranar 12 ga watan Mayu na cewa "zaben bai kammalu ba" wanda hakan ya sanya aka saka sabuwar ranar maimaita zaben.

Wani mai sanya idanu a kan harkokin zabe a karamar hukumar Chikun, Moses Dangana, ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sabuwar na'ura mai kwakwalwa ta kada kuri'a tana da matukar muhimmanci inda ya kara da cewa "mene yasa tun a baya ba'a amfani da ita don magance magudin zabe."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel