An kama sojan bogi dauke da katin shaidan jami'in 'dan sanda

An kama sojan bogi dauke da katin shaidan jami'in 'dan sanda

An gurfanar da wani mai aikin karrafa, Victor Nyaku, a gaban wata kotun Majistare da ke Ikeja a Legas bisa laifin yin sojan gona tare da yiwa wani dukka.

Ana tuhumar Nyaku mai shekaru 47 da laifin gabatar da kansa a matsayin jami'in soja sanye da khakin sojin Najeriya kuma an same shi dauke da katin shaidan jami'in na sanda wanda ba nashi ba ne.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Godwin Awase ya shaidawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Afrilu a Anifowoshe da ke Ikeja a Legas.

Wani sojan gona ya yabawa aya zaki bayan ya shiga hannu a Legas
Wani sojan gona ya yabawa aya zaki bayan ya shiga hannu a Legas

Ya ce wanda ake tuhumar yana sanya da khakin sojin Najeriya inda ya ke gabatar da kansa a matsayin soja duk da cewa bai taba aiki da Hukumar sojin ba.

KU KARANTA: An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

"Wanda ake tuhumar yana tuka motarsa kirar Toyota Camry ne kuma ya toshe hanyar da wata babban motar fasinjoji (BRT) za ta wuce kuma ya bukaci direban babban motan ya yi ribas don ya wuce.

"Direban babban motan ya kasa yin ribas din saboda motarsa tana da tsawo sosai, hakan yasa wanda ake zargin ya sako daga motarsa dauke da dorina kuma ya fara zane direban babban motan.

"Hayaniyan ya janyo hankalin yan sanda kuma bayan sun iso wajen suka bukaci su ga katin shaidar ko shi wanene.

"Wanda ake tuhumar da ke sanye da kayan soja ya nuna musu katin shaidan dan sanda dauke da wata suna ba wanda ya fada musu ba."

Hakan yasa suka gano cewa sojan gona ne kuma suka tafi dashi caji Ofis, a can ne ya fada musu cewa ya sayi khakin sojan ne a gwanjo kuma wani ne ya bashi katin shaidan dan sandan a Ikeja.

Laifin da ya aikata ya yi karo da sashi na 171 da 380 da 382 na dokar masu laifi na shekarar 2015 na jihar Legas.

Nyaku ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa hakan yasa alkali ya bayar da belinsa kan kudi N100,000 kuma ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel