Rikici na neman barkewa a majalisa kan shugaba Buhari

Rikici na neman barkewa a majalisa kan shugaba Buhari

Wasu 'yan majalisu a Najeriya sunyi wasu maganganu da suka jawo hankulan majalisar wakilan kasar nan, saboda sun sanarwa da manema labarai cewar basu ji dadin matakin da majalisun biyun suka dauka akan shugaban kasa Buhari ba

Kawunan 'yan majalisu ya rarrabu akan shugaba Buhari
Kawunan 'yan majalisu ya rarrabu akan shugaba Buhari

Wasu 'yan majalisu a Najeriya sunyi wasu maganganu da suka jawo hankulan majalisar wakilan kasar nan, saboda sun sanarwa da manema labarai cewar basu ji dadin matakin da majalisun biyun suka dauka akan shugaban kasa Buhari ba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace wani ma'aikacin INEC a wata jiha

Hakan nema yasa majalisar wakilai ta 'ya'yanta biyu Aldulmummuni Jibrin da kuma Muhammadu Gudaji Kazaure ga kwamitin binciken saboda suna zargin cewa ana yin taron ne akan yunkurin tsige shugaba Muhammadu Buhari. Sun tabbatar da cewar tuni suka fara daukar sunayen 'yan majalisun da suke da ra'ayin tsige shugaban kasar.

Honarabul Lawal Yahaya Gumau yayi tsokaci akan cewar idan ma ace shugaba Buhari yayi wani laifi ne kamata yayi ace kowacce majalisa tayi zaman ta daban, kafin daga baya su zo su zauna suyi muhawara a junansu akan lamarin. Yace duk wadannan maganganun da ake yi magana ce data shafi hukumar 'yan sanda da shugaban majalisar dattawa.

A cewar Gumau din yace bisa dukkan alamu ana so ayi amfani da majalisun biyu ne domin su goyi bayan shugaban majalisar dattawa. Wani yunkurin kuma shine ana so ace dole akwai hannun shugaba Buhari akan matsalar Bukola Saraki da hukumar 'yan sanda. Yace iya abinda suka sani shine babu ruwan shugaban kasa da rigimar Saraki da 'yan sanda. Idan har yana da gaskiya babu yadda za'ayi Buhari ya saka 'yan sanda su ci masa mutunci.

Sanata Abdullahi Yahaya shi ma ya ce bai kamata a dauko lallurar wani ba ta zama ta majalisa. Wadanda aka kai kotu ba wannan gwamnatin ba ce ta kaisu. Barnar da suka yi ne tun lokacin gwamnatocin Obasanjo da ‘Yar’Adua amma kotunan ne basu yi aikinsu ba aka sake farfado da maganar yanzu. Duk wanda ake zarginshi da cin kudin jama’a ya je kotu ya kare kansa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel