An yi ma Dansandan dake Tafsirin Qur’ani karin girma zuwa Kwamishinan Yansanda
Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya yi ma wani jajirtaccen jami’in Dansanda, Ahmad Abdulraman karin girma zuwa mukamin kwamishinan Yansanda, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Hayatuddeen Lawal Makarfi ne ya bayyana haka a shafinsa, inda ya tabbatar da labarin karin girmar da hukumar Yansandan Najeriya ta amince a yi ma Dansanda Ahmad.
KU KARANTA: Soyayyar Uba da Da: Wani tsautsayi mai ban tausayi ya faru da wani Uba da Dansa
Shi dai Ahmad shi ne jami’in Dansanda daya tilo da ya yi fice wajen gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani a watan Azumin Ramadan a jihar Kaduna, inda yake gabatar da Tafsirin a shelkwatar Yansandan jihar Kaduna.
A baya Legit.ng ta kawo muuku rahoton cewar Kwamishina Ahmad Abdulrahman yace ya samu kwarin giwar shiga aikin Yansanda ne daga mariyagin Shehin Malami, Abubakar Mahmud Gumi, bayan rikicin addini da ya kaure a zangon kataf na jihar Kaduna.
Da fatan Allah yayi ma sabon mukaminsa albarka, tare da amfanar da al’umma gabaki daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
https://www.youtube.com/watch?v=FMiXNSPhBlo
Asali: Legit.ng