Wani Basarake da ya musulunta ya daga Yayansa mata da Matansa 11 ga duk mai son ya aura

Wani Basarake da ya musulunta ya daga Yayansa mata da Matansa 11 ga duk mai son ya aura

Wani Basarken gargajiya daga kabilar Gwari ta jihar Kaduna ya nemi matasan Musulmai da su taimaka su garzayo gidansa domin neman auren yayansa da wasu daga cikin Matayensa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wanna Basarake mai suna Dauda Auta ya bayyana haka ne a lokacin da ya Musulunta a hannun fitaccen Malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, a Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna.

KU KARANTA: Soyayyar Uba da Da: Wani tsautsayi mai ban tausayi ya faru da wani Uba da Dansa

Malam Dauda yayi wannan kira ne duba dacewa ya Musulunta, don haka ya zama wajibi a gareshi ya rabu da wasu daga cikin Matansa na aure guda 11, don ya dace da Mata 4 da addinin Musulunci ya tanadar.

Wani Basarake da ya musulunta ya daga Yayansa mata da Matansa 11 ga duk mai son ya aura
Dauda

Haka zalika Dauda ya bayyana cewar yana da yaya dai dai har guda arba’in da hudu, 44, don haka ne yake kira ga matasa Musulmai dake da niyyar aure su auri balagaggun yayansa Mata.

Wannan tallar yaya mata da Malam Dauda yayi ba wani sabon abu bane a al’ummar Arewacin Najeriya, inda wasu mata ko kuma iyayensu ke amfani da wannan hanya wajen nema ma kansu ko yayansu mazajen aure nagari.

Da fatan Allah ya sa yayan Malam Dauda da Matayensa su samu mazaje na nagari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel