Wani fasinja ya shiga jirgin sama jakar shi cike da macizai da kunamu

Wani fasinja ya shiga jirgin sama jakar shi cike da macizai da kunamu

A tashar sauka da tashin jiragen sama na birnin Santambul a kasar Turkiyya an bankado jakar wani fasinjan jirgi dauke da wasu nau'i na dabbobi masu yawan gaske cikin su kuwa harda macizai da kunamu masu rai

Wani fasinja ya shiga jirgin sama jakar shi cike da macizai da kunamu
Wani fasinja ya shiga jirgin sama jakar shi cike da macizai da kunamu

A tashar sauka da tashin jiragen sama na birnin Santambul a kasar Turkiyya an bankado jakar wani fasinjan jirgi dauke da wasu nau'i na dabbobi masu yawan gaske cikin su kuwa harda macizai da kunamu masu rai.

DUBA WANNAN: An kama wani mutum yayi wa 'yar shekara 9 fyade a jihar Sokoto

Rahotanni sun nuna cewar kasar Rasha ce ta aiko da wannan jakar zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya, saboda sun rasa mai jakar.

Hukumar kwastam ta kasar Turkiyya sune suka binciko wannan jaka, inda suka yi amfani da na'ura mai gani har hanci wato X-ray, a binciken nasu sun gano nau'in dabbobi har guda 9 wadanda suka hada da macizai da kunamu, kwadi, kunkuru, 'ya'yan kada, kadangaru da dai sauran dabobbi.

An tabbatar da cewar jakar ta wani dan kasar Rasha ce wanda ya fito daga birnin Vietnam. A karshe dai hukumar ta mika dabobbin ga ma'aikatar noma da kiwo ta kasar Turkiyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng