Kidan yaki: Wani dan takaran gwamna ya roki Buhari ya koya masa yadda ake kauce ma harbin bindiga
Ministan albarkatun kasa, Kayode Fayemi ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koya masa yadda ake kauce ma harsashi idan harbo shi sakamakon cewa tsohon Soja ne shi, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kayode ya bayyana haka ne a yayin taron majalisar zartarwa daya guda a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni a fadra shugaban kasa, inda ya bayyana ma mahalarta taron matakinsa na yin murabus daga gwamnatin Buhari.
KU KARANTA: Alhinin rabuwa: A yau marigayi Ado Bayero ya cika shekaru 4 da rasuwa
Kayode wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti dake tafe, yayi murabus ne da nufin neman cika burinsa na sake lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.
A satin daya gabata ne dai Fayemi ya sha da kyar bayan wani Dansanda yayi yunkurin kashe shi a yayin wani taron karramawa da aka shirya masa a sakatariyar jam’iyyar APC na jihar Ekiti dake unguwar Ajilosun, cikin garin Ado Ekiti.
A sakamakon wannan harbe harbe da aka yi a wajen, tsohon dan majalisa kuma hannun daman Kayode na can cikin mawuyacin hali bayan da wani harsashi ya same shi, tare da wasu mutane guda biyar.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar wani dansanda ne ya harba bindigar, amma ya shiga hannu daga bisani, kuma yaci na jaki a hannun jama’a har sai da suka kusan kashe shi, a yanzu haka rundunar Yansandan Najeriya ta sallame shi daga aiki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng