Saraki da Dogara sun dinke bakunansu akan kujerun marigayi Wakili, Bukar da Jibrin
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun like bakunansu kan dalilin da yasa ba’a neman wadanda zasu maye gurbin yan majalissun da suka mutu watannin baya.
Har yanzu tallata kujerun Sanata Malam Ali Wakili (APC, Bauchi), Sanata Bukar Mustapha (APC, Katsina) da na dan majalisa Buba Jibril (APC, Kogi) domin ba hukumar zabe mai zaman kanta damar shirya zabe ba.
Wakili ya rasu a ranar 17 ga watan Maris, dan majalisar wakilai Buba Jibril ya rasu a ranar 30 ga watan Maris sannan kuma Mustapha ya rasu a ranar 4 ga watan Afrilu.
Anyi jimamun mutuwar nasu amma majalissun biyu basu sanar da hukumar zabe mai zaman kanta komai ba wanda zai basu damar fara shirin zabar sabbin yan majalisa domin maye gurbin wadanda suka rasun.
A lokacin da majiyarmu ta tuntubi Sanata Aliyu Sabi Abdullahi kan batun bai tofa komai ba.
Wata majiya a majalisar dokokin ta bayyana cewa suna jiran umurni daga shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki kafin a dauki mataki.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar EFCC ta gurfanar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi da wasu mutane 4 a gaban kotu (hotuna)
Har ila yau da aka tuntubi kakakin Saraki, Yusuph Olaniyonu yace baida abun fadi akan lamarin.
A halin da ake ciki, majalisar dokokin kasar ta gindaya wasu sharuda da take son shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika ko kuma su tsige shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng