Alhinin rabuwa: A yau marigayi Ado Bayero ya cika shekaru 4 da rasuwa

Alhinin rabuwa: A yau marigayi Ado Bayero ya cika shekaru 4 da rasuwa

Ikon Allah, rai bakon Duniya, kwanci tashi har tsohon Sarkin, Ado ya cika shekaru hudu da rasuwa, inda rasu a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 2014 yana mai shekaru 83, bayan jinya da ya sha fama da ita, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

An haifi marigayi Ado Bayero a shekarar 1930, kuma iyayensa suna Sarki Abdullahi Bayero da Hajiya Hasiyatu. Sarki Ado yana rike da mukamin jakadan Najeriya a kasar Sanigal a lokacin da Sir Ahmadu Bello Sardauna ya nada shi Sarki a ranar 22 ga watan Oktoban 1963, inda ya zama Sarki na 13 tun bayan jihadin Danfodio.

KU KARANTA: Kashedi: Sule Lamido yace sama zata fado a duk ranar da BUhari ya kama Joathan

Sarakai biyu da suka mulki jihar Kano kafin Ado Bayero sun hada da Sarki Muhammadu Sunusi mai murabus, wanda aka tsige shi, sai Muhammadu Inuwa ya gaje shi, wanda ya kwashe watanni uku kacal yana mulki kafin ya rasu, daga nan sai Ado Bayero, inda shi ma Sunusi Lamido Sunusi ya gaje shi bayan rasuwarsa.

Alhinin rabuwa: A yau marigayi Ado Bayero ya cika shekaru 4 da rasuwa
Ado Bayero

Kafin zamansa Sarkin Kano, Ado cikakken dan kasuwa ne, kuma yayi aikin banki, yayi aikin dan doka, ya taba zama dan majalisa, sa’annan kwararren masanin dangantakar kasa da kasa, Ado ya shahara a tsakanin attajirai da talakawa.

Sai dai a zamaninsa an taba kai masa, inda ya tsallake rijiya da baya a wani hari da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kai masa, wanda yayi sanadin mutuwar dogarinsa da direbans,a yayansa biyu kuma suka jikkata.

Hakazalika ya fuskanci barazana daga gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abubakar Rimi, wanda ya yanke wani kaso daga masarautar Ado, sa’annan ya hana hakimai da dagatai kai masa gaisuwa, bugu da kari gwamnati ta taba sanya masa takunkumi a shekarar 1984.

Marigayi Ado Bayero ya kwashe shekaru 51 yana mulkin Kano kafin rai yayi halinsa, da fatan Allah ya jikansa da gafara

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel