Za mu yi kokari mu rage gurbatar da wurare da man fetur - NNPC

Za mu yi kokari mu rage gurbatar da wurare da man fetur - NNPC

- NNPC tace za ta dabbaka wasu tsare-tsare domin kawo gyara a aikin ta

- Hukumar na kokarin rage gurbata wurare da ake yi wajen aiki da fetur

- NNPC dai ta bayyana wannan ne jiya a wajen wani taro na musamman

Mun samu labari dazu daga Daily Trust cewa Hukumar man fetur na Najeriya na NNPC ta kawo wani sabon tsari da zai taimaka wajen rage barna da kuma kawo kazanta a wuraren da ake aikin mai a Kasar.

Za mu yi kokari mu rage gurbatar da wurare da man fetur - NNPC
Shugaban Kamfanin NNPC na kasa Maikanti Baru

Shugaban Kamfanin NNPC Dr. Maikanti Baru ya bayyana cewa NNPC za ta rage kazantar da aka saba wajen aikin man fetur tare da dabbaka wasu tsare-tsaren da su sa a rage watsar da dattin mai. Baru ya bayyana wannan ne jiya a Abuja.

Rahoton ya zo mana cewa wani babban Jami’in kula da aikace-aikace na Hukumar NNPC watau Injiniya Saidu Muhammadu ne ya wakilci Maikanti Baru a wajen wannan taro na musamman a babban ofishin NNPC da ke babban birnin Tarayya.

KU KARANTA: Ministan Buhari yayi buda-baki gidan Dahiru Bauchi

NNPC tace za ta tafi da tsarin da ta kawo na rage kazanta a Kasar wanda hakan zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma. Robobi dai na da illa ga ruwa da kuma kasar da jama’a ke amfani da ita don haka NNPC tace za ta yi gyara a aikin ta.

Hukumar na NNPC tayi wannan taro ne a jiya Talata da ta ke Ranar bikin muhalli na Duniya. NNPC za tayi amfani da fasahar zamani domin ganin an rage kazanta da kuma gurbata wuraren da al’umma su ke zama domin gudun cutuwa.

Kwanaki Majalisar Kasar nan za tayi bincike game da wasu kudi da ake zargi su na yawo a kamfanin main a NNPC wanda sun haura Naira Biliyan 32. Sanata Dino Melaye ya kawo wannan kudirin a Majalisa inda aka yi na’am da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel