Al’ajabi: Wata yarinya ta dawo gida bayan shekara biyu da mutuwa, an samu itace bayan tone kabarin ta

Al’ajabi: Wata yarinya ta dawo gida bayan shekara biyu da mutuwa, an samu itace bayan tone kabarin ta

- Wata yarinya da aka tabbatar da mutuwar ta, ta dawo gida bayan shekara biyu

- Iyayen yarinyar sun shiga halin dimuwa bayan yarinya ta dawo gida tare da shiadawa iyayenta cewar an binne itace ne a madadin ta

- An fara gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar labrin da yarinyar ta bayar

Dangin wata yarinya da ta dawo gida bayan mutuwar ta da shekaru biyu sun shiga halin dimuwa da mamaki. An bayyana cewar yarinyar ta mutu shekaru biyu da suka wuce a garin Ndola dake kasar Zambia bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Al’ajabi: Wata yarinya ta dawo gida bayan shekara biyu da mutwa, an samu itace bayan tone kabarin ta
Wata yarinya ta dawo gida bayan shekara biyu da mutuwa

Rahotanni sun bayyana cewar an kai gawar yarinyar mai suna Winnie dakin ajiyar gawa na wani asibiti kafin daga bisani a binne ta a wata makabarta dake Mitingo.

Sai gas hi yarinyar ta dawo gida bayan shekaru biyu da mutuwar ta tare da shaidawa dangin tad a jama’a dake cikin halin kaduwa cewar, an binne itacen ayaba ne a madadin ta a lokacin da aka bayyana cewar ta mutu.

DUBA WANNAN: Mahaukata ne suka kewaye shugaba Buhari - Sheikh Gumi

Majiyar Legit.ng ta bayyana mata cewar an gayyato jami’an ‘yan sanda domin binciken wannan abun mamaki. Dangin yarinyar sun bukaci a gudanar da gwajin kwayoyin halitta a kan yarinyar.

Hukumar ‘yan sanda ta bukaci a gabatar mata da takardun shiadar haihuwa da na mutuwar Winnie domin cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel