Ga Buhari ga Atiku: Ministan Buhari ta yi tsayuwar gwamen Jaki

Ga Buhari ga Atiku: Ministan Buhari ta yi tsayuwar gwamen Jaki

A yayin da zaben shekarar 2019 ke karatowa, kowanne dan siyasa na neman tudun dafawa da zai kaisa ga gaci, kamar yadda bahaushe ke cewa kowanne Allazi da na sa Amanu, sai dai a nan, Ministan al’amuran Mata, Aisha Alhassan na cikin tsaka mai wuya.

Legit.ng ta tabbatar cewa sanannen abu ne tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ne maigidan Aisha Alhassan, ya yi dawainiya da ita sosai, amma a yanzu shugaban kasa Muhamamdu Buhari ne maigidanta a gwamnantance.

KU KARANTA: Wata Annoba ta hallaka daliba 1, ta kwantar da 40 a kwalejin yan Mata na Kaduna

Idan za’a tuna a shekarar data gabata ne aka hangi Ministar a gidan Atiku tana tabbatar masa da mubaya’a, inda tace ta yi alwashin ba zata goyi bayan shugaba Buhari ba koda zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019, a cewarta Atiku zata mara ma baya.

Ga Buhari ga Atiku: Ministan Buhari ta yi tsayuwar gwamen Jaki
Buhari, Aisha da ATiku

Sai dai a yan kwanakin nan kuma sai aka jiyo Minista Alhassan tana cewa 2019 sai babu Buhari, inda take karawa da cewa gwmanatin APC za ta cigaba da mulkin Najeriya din din din har sai Mahadi ya bayyana.

“Duk wanda ya tsaya takara da Buhari zai bata lokacinsa ne kawai, don kuwa Buhari zai lashe zaben shugaban kasa a 2019, kuma APC zata mulkin Najeriya na dindindin, nima zan sake tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba.” Inji ta.

Da wannan a iya cewa Aisha ta shiga tsaka mai wuya, don kuwa zata bi Atiku ne dake neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ko kuwa za ta bi Buhari dake jam’iyyar APC, domin a yanzu haka tsayuwar gwamnen Jaki ta yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng