Kishi ya saka wata mata yi wa kishiyar ta wanka da tafasashen ruwa
A yau Talata ne aka gurfanar da wata mace mai suna Grace Azagba mai shekaru 51 gaban kotun majistare da ke Ikeja saboda watsa wa kishiyarta tafashashen ruwa.
An gurfanar da Azagba ne tare da dan ta mai shekaru 14 bisa tuhumarsu da aikata laifuka biyu na hadin baki da kuma raunana mutum.
Wadda ake tuhumar da ke zaune a Abule-Egba a Legas ta musanta aikata laifukan da ake tuhumar ta da aikatawa.
KU KARANTA: Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Ezwkiel Ayorinde ya shaidawa kotu cewa wanda ake tuhumar ta aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Mayu a gidansu da ke Abule-Egba.
Ya ce wanda ake tuhumar da antayawa kishiyarta, Mrs Marina Azagba ruwan zafi wanda hakan ya haifar mata da raunuka a jiki.
"Wanda ake tuhumar ta daye wa kishiyarta jiki da ruwan zafi," inji shi.
Ayorinde ya ce wanda ta shigar da karar ta dade tana fuskantar ukubu da wahalwalu daga wanda ake tuhumar da yaranta tun shekaru biyu da suka shude bayan an auro ta.
"Kishiyoyin biyu sun kasance suna zaman doya da manja ne tunda amaryar ta tare a gidan shekaru biyu da suke shude.
"Wanda ake tuhumar ta sha nakada wa mai shigar da karar duka lokuta da dama wanda hakan ya janyo mata kunci a rayuwarta.
"Mai gidansu ya yi kokarin sasanta su amma hakan bai yiwu ba.
"A ranar da abin ya faru, kishiyoyin sunyi musayar maganganu kamar yadda suka saba amma sai wanda ake tuhumar da dako ruwan zafi ta watsa wa mai shigar da karar.
"Mai gidansu ya kai kara zuwa ofishin yan sanda wanda hakan ya janyo aka damke wanda ake tuhumar, ita kuma mai shigar da karar tana asibiti tana karbar magani," inji shi.
Laifukkan sun saba wa sashi na 245 da 411 na dokar masu aikata manyan laifuka na shekarar 2015 na jihar Legas.
Alkalin kotun, Mrs. B.O Osumsanmi ta bayar da belin wanda ake zargi da dan ta a kan kudi N300,000 kowannen su tare da mutane biyu wanda za su tsaya musu.
An kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Yuli.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng