Wata Mata ta Kashe Mijin ta daga yiwa Kyanwar su Duka
Wani mummunan rahoto mai tattare da ban al'ajabi da shafin jaridar The Punch ta ruwaito ya bayyana cewa, ana zargin wata Mata da aikata babban laifi na harbe Mijinta murus wai don kurum ya dauke salo na sabon lakadawa kyanwar su duka.
Ana zargin Mary Harrison mai shekaru 47 a duniya da laifin kashe Mijin ta, Dexter Harrison a mazaunar su da Fall Manor Drive dake birnin Dallas na garin Texas a Kasar Amurka.
Mary dai ta shaidawa jami'an tsaro cewa a birnin Dallas cewa, ta harbe Mijin na ta dan shekara 47 a duniya a yayin wata sa'insa da ta shiga tsakanin su a ranar Asabar din makon da ya gabata.
Legit.ng ta fahimci cewa, Mary ta shaidawa jami'an cewa Mijin na ta ya saba kai hannu kan Kyanwar su wanda wannan lamari ya dade yana ci ma ta Tuwo a Kwarya.
Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Mista Harrison zuwa wani Asibiti na kurkusa inda a nan ya ce ga garin ku nan.
KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun cafke wasu Mutane 3 masu garkuwa da Mutane sanye da Kakin Sojin Kasa a Jihar Osun
Makwabta sun labartawa jami'an tsaro cewa a kwana-kwanan nan aka nemi wannan Kyanwa aka rasa yayin da ta yi kaura a sanadiyar duka da ta ke yawan sha a hannun Marigayi Dexter.
A sanadiyar haka ne Mary ta bayar da cigiyar wannan Kyanwa watakila ko ta fada cikin kyakkyawan hannu, inda ana zauna kwatsam sai shawagi ya kado ta gida.
A halin yanzu dai Kotu ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wannan Uwargida sakamakon danyen hukuncin da ta yanke, inda ta yi ma ta goma ta arziki na bayar da belin ta akan zunzurutun kudi na Dalar Amurka 100, 000.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng