A yau ne dokar karin kudin harajin giya da taba zata fara aiki a Najeriya

A yau ne dokar karin kudin harajin giya da taba zata fara aiki a Najeriya

A yau ne sabon harajin kudin giya dana taba zai fara aiki, inji wata majiya mai karfi. Majiyar tace ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan sabon tsarin harajin a yau, wanda zai fara nan da kwanaki 90

A yau ne dokar karin kudin harajin giya da taba zata fara aiki a Najeriya
A yau ne dokar karin kudin harajin giya da taba zata fara aiki a Najeriya

A yau ne sabon harajin kudin giya dana taba zai fara aiki, inji wata majiya mai karfi. Majiyar tace ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu akan sabon tsarin harajin a yau, wanda zai fara nan da kwanaki 90.

DUBA WANNAN: Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

Duk da babu kari akan harajin kayan da ake sarrafawa a gida, shugaban kasar ya bada wa'adin kwanaki 90 kafin sabon tsarin ya fara aiki.

Ministan kudi, Mrs Kemi Adeosun, ta fadi sabon tsarin harajin giya dana taba sigarin a matsayin matakin gwamnati na rage matsalolin rashin lafiya da ke tattare da taba da giya.

Tayi bayanin cewa sabon tsarin harajin zai yi aiki ne na tsawon shekaru 3, wanda zai fara daga shekarar 2018 zuwa 2020 don ya daidaita tasirin farashin kayan.

A karkashin sabon tsarin harajin taba sigarin, a karin kashi 20 cikin dari, duk karan sigari daya zata samu karin naira 1 a 2018, naira biyu a duk kara daya a 2019 da Naira 2.90 a duk kara daya a 2020.

Sabon tsarin giya kuma zai shafi Beer, stout, wines da spirits na shekara 3,daga 2018 zuwa 2020.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel