Yaba kyauta tukuici: Yadda wasu daliban Firamari ke yi ma Buhari addu’a kulliyaumin

Yaba kyauta tukuici: Yadda wasu daliban Firamari ke yi ma Buhari addu’a kulliyaumin

A sakamakon tsananin soyayyar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake zukatan yan Najeriya, ciki har da kananan yara, hadi da kyawawan ayyukan cigaba dayake kai ma al’ummomin kasar nan daban daban ta sanya Buhari samun kyawawan addu’o’i.

Daily Trust ta ruwaito daliban makaratun firamari musamman wadanda suke amfana da tsarin ciyarwa na gwamnatin tarayya suna yi ma shugaba Buhari addu’ar samun nasara a kullum kafin su fara cin abinci.

KU KARANTA: An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’in kula da ciyarwar a jihar Bauchi, Aliyu Muhammad Sani ya bayyana cewar wannan addu’ar da daliban firamari ke yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wai ya kadaita bane kadai a garin Bauchi, “A’a a kafatanin makarantun Firamari na jihar Bauchi ma ana yi masa addu’a.” Inji shi.

Yaba kyauta tukuici: Yadda wasu daliban Firamari ke yi ma Buhari addu’a kulliyaumin
Daliban

Sai dai wannan addu’a ta kananan yara masu karancin zunubai ba ta tsaya kadai akan shugaba Buhari ba, inda shi ma gwamnan jihar yana samun kyawawan addu’o’I daga garesu.

Game da wannan, Malam Muhammadu Sani yace iyayen dalibai, malamansu da kuma jami’an ilimi a matakin kananan hukumomi ne suka kirkiro tsarin yi ma shuwagabannin addu’a sakamakon kokarin da suke yi na inganta rayuwansu.

Idan za’a tuna a farkon mulkin gwamnatin shugaban kasa Buhari ne ta kirkiro tsarin ciyar da daliban Firamari don janyo hankulan yara kanana zuwa makaranta, magance cutar rashin sinadari mai kyau a jikin yara, samar da ayyukan yi da kuma inganta tattalin arzikin kasa, inda jihar Bauchi ta cika dukkanin sharuddan da ake bukata wajen zabar jihohin da zasu fara cin moriyar wannan tsari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng