Mutuwar matashin Musulmi Ali Banat: Duba hotunan irin yadda ya taimakawa Musulmai a Maiduguri
Allah ya yiwa matashin baturen Musulmi dan kasar Australia, Ali Banat, mai gidauniyar taimakon Musulmi masu karamin karfi dake fadin duniya, rasuwa.
Matashin ya mutu ne bayan kamuwa da cutar daji da ake kira Cancer a Turanci.
Kafin mutuwar sa, matashin ya fara gina wasu muhalli ga muslmai da suka tsinci kan su cikin mayuwacin hali sakamakon rikicin Boko Haram a jihar Borno.
Bayan gina muhalli ga ‘yan sansanin gudun hijira, Marigayi Ali Banat, kan samu lokaci domin kasancewa tare da yara dake sansanin da kuma yin wasa das u ko cin abinci tare.
Akwai kimanin ‘yan Najeriya mutum miliyan biyu a sansanin ‘yan gudun hijira dake garuruwa da unguwannin garin Maiduguri da dama.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan ta'adda da hukumar 'yan sanda ke zargin Saraki da daukan nauyin su
Kungiyoyi da kasashe na bayar da tallafin kayan abinci, masarufi da magunguna domin inganta rayuwar mazauna sansanin ‘yan gudun hijira. Akwai zargin almundahana da karkatar da kayan da gwamnati kan saya domin rabawa ga ‘yan sansanin na gudun hijira.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng